<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>322</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Yanzu kun gama yaƙinku.
 Kun kwance dukan ɗaurarru,
 Kun ba da su ga Allahnku.
 Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Gun Yesu za ku huta yau.

[V2]
 2) Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Kun kai ga burinku yanzu.
 Ba yunwa, babu ƙishiruwa,
 Ba wuyar hanya, ba gajiya.
 Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Yesu ya shirya gidanku.

[V3]
 3) Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Barci ya kwashe jikinku,
 A ƙarewa Ɗan Allah kuwa
 Zai raya ku da nasara.
 Ya tsarkaka na Allahnmu,
 Ga hasken Yesu wurinku.

[V4]
 4) Ya Allahnmu na tsarkaka,
 Muna roƙo a wurinka.
 Albarka ga Ubangiji
 Da Ruhunsa Mai Tsarki.
 Ka sada mu da tsarkaka,
 Ka kai mu wurin zamanka.</lyrics>
<title>Ya Tsarkaka Na Allahnmu LW322</title>
</song>